12 Satumba 2026 - 23:00
Source: ABNA24
Gaza: Ci Gaba Da Hare-Haren Mamaya.. Hukumar Kare Fararen Hula Ta Ciro Gawar Shahidai 13

Isra'ila tana kai hare-hare a wurare daban-daban a Zirin Gaza, Motar aiki ɗaya kawai ta ke aiki don ciro dubban gawawwaki’ Hukumar Kare Fararen Hula ta Gaza tana fuskantar babban aiki

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA – ya ruwaito cewa: Hukumar Kare Fararen Hula ta Gaza ta bayyana cewa ƙungiyoyinta sun ciro gawar shahidai 13 daga ƙarƙashin tarkace cikin ranar Asabar, ciki har da gawar shahidai 8 daga yankunan Zaytoun da Yarmouk na birnin Gaza, da shahidai 5 daga sansanin Nuseirat na lardin tsakiya.

Mamayar Isra'ila na ci gaba da hare-harenta kan Zirin. An ji wa wani dattijo rauni daga harsashin "sojojin" mamayar a yankin Beit Lahia a arewacin Zirin.

A cikin sa'o'in da suka gabata, motocin Isra'ila sun harba harsasai a gabashin garin Al-Qarara a arewacin birnin Khan Younis, kudancin Zirin.

Sanna Isra’ila ta jefa bama-bamai masu ƙara a sararin gabashin birnin Gaza, inda unguwar Shujaiya ma ta sha fama da harbin manyan bindigogi. Haka kuma manyan bindigogin mamayar sun kai hari yankunan arewacin Bureij, tsakiyar Zirin Gaza.

Shahidai 1,369 Tun Bayan Sanarwar "Dakatar da Wuta"

A wani lokaci a baya a yau, Ma'aikatar Lafiya ta Falasɗinawa a Gaza ta bayyana isowar shahidai sabbin 10 da raunuka 56 zuwa asibitocin Zirin cikin sa'o'i 48 da suka gabata, sakamakon ci gaba da mamayar Isra'ila.

Ma'aikatar ta yi nuni da cewa jimillar waɗanda sukai shahada tun bayan sanarwar "dakatar da wuta" a ranar 11 ga Oktoba ta kai shahidai 1,369, yayin da adadin waɗanda suka ji rauni ya kai 4,627, tare da ciro gawar shahidai 831.

Dangane da ƙididdigar gaba daya, adadin waɗanda sukai shahada tun farkon mamayar Isra'ila kan Zirin Gaza a ranar 7 ga Oktoba 2023 ya ƙaru zuwa shahidai 73,783, yayin da adadin waɗanda suka ji rauni ya kai 174,738.

Wannan yana zuwa ne yayin da mamayar ke ci gaba da karya "yarjejeniyar tsagaita wuta", inda "sojojinta" ke harbi a yankunan Zirin da harsashin manyan bindigogi, da hare-hare ta sama da jiragen yaƙi marasa matuƙa, tare da rushe unguwannin zama da ababen more rayuwa, da kashe fararen hula.

……………………..

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha