Wata sanarwa daga ‘yan sandan kasar na cewa wani mutun mai kimanin shekaru 34 ya aikata harbe-harben.
Sanarwar ‘yan sandan na cewa an jikkata maharin a lokacin da ‘yan sanda ke kokarin kama shi yana shirin tserewa don barin gidan rawan amma kuma daga bisani ya mutu a asibiti.
Wannan hari na zuwa ne kwanaki biyu bayan wani harin da wani mutun dauke da wuka ya kai shagon saida kayayyaki inda aka sami hasarar rayuka a garin Hamburg