Gidan levision na Presstv a nan Tehran ya nakalto Mahmood Aliwi yana fadar haka a jiya Asabar, ya kuma mkara da cewa bayan hare haren na Tehran a ranar laraban da ta gabata , dan ta'addan da ya shirya hare haren ya arce ya bar kasar, amma tare da taimakon hukumomin leken asiri na kasashen waje an kashe shi a wajen kasar a jiya Asabar. Ministna bai bayyana kasar da ta taimakawa wajen kashe dan ta'addar ba.
Mutane sama 17 suka yi shahada a hare haren da yan ta'adda 5 suka kai a majalisar dokokin kasar Iran da kuma haramin Imam Khomaini (q) a nan birnin Tehran. Sannan wasu 52 kuma suka ji rauni.
Kungiyar yan ta'adda ta Daesh ta dauki alhakin kai hare haren na Tehran. Daga karshe ministan ya kammala da cewa a cikin yan watannin da suka gabata sun sami nasara hana shirye shiryen kai harin ta'addanci hau sau 25 a duk fadin kasar.288