31 Janairu 2017 - 15:28
Gwamnati bata daukaka kara kan kin sakin Sheikh El-Zakzaky ba

Rahotanni da suke fitowa daga majiyoyi masu tushe sun karyata labaran da wasu daga cikin jaridun kasar nan suka dauka a baya na cewa, wai gwamnati ta daukaka kara kan kin sakin jagoran Harkar Musulunci a Nigeria Sheikh Ibraheem Yaqoub El-Zakzaky da kuma ci gaba da rike shi da jami'an tsaron DSS suke yi.........

Rahotannin sun tabbatar da cewa wadan can labaran da aka yada ba su da tushe balle makama, bayan binciken da lauyoyin da ke kare Sheikh El-Zakzaky suka yi kuma suka tabbatar da cewa babu wani abu mai kama da hakan.

Wasu daga cikin iyalan Malam suma sun tabbatar da hakan a lokacin da suke karyata labaran da kuma kara nuna cewa mai yiwuwa hukuma ta yada wadan can labaran ne saboda ta kare kanta ta nunawa duniya ita ma tana bin doka da oda.

Kamar dai yadda aka sani ne yau sama da shekara daya ke nan tun bayan kisan kiyashi da sojoji suka yi a Husainiyar Baqiyyatullah da kuma gidan Malam a Gyallesu ake tsare da Sheikh El-Zakzaky da iyalin sa Malama Zeenatuddeen Ibraheem a hannun jami'an hukumar DSS ba tare da an gabatar da shi kotu ba.288