3 Janairu 2017 - 15:39
Nan Ba Dadewa Ba Za'a Murkushe Kungiyar ISIS - Shugaban Faransa

Shugaban Faransa Francosi Hollande, yayi alwashin cewa nan bada jumawa ba za'a sami galaba kan kungiyar ISIS. Holland yayi wanan furucin ne lokacinda ya kai ziyarar wuni daya a a Iraqi,a ranar kuma wani dan kunar bakin wake ya kai kari a wata kasuwa a Bagadaza, ya halaka mutane 32.

"Deash tana tsamurewa.Kuma za'a yi galaba akanta," inji Holland, ya kira kungiyar da lakabin da ake kiranta da labaraci.

Sa'o'i bayanda Holland isa Iraqi a jiya Litinin, bam ya tashi a wata kasuwa dake unguwar Sadr dake gabashin birnin dake shake da leburori. Kungiyar ISIS ta dauki alhakin kai harin.

A lokacin da suka yi taro da menama labarai tareda shugaban na Faransa, PM Iraqi Haider al-Abadi, yace maharin ya shigo kasuwar a zaman wand a yake son ya dauki lebori aiki, daga nan ne ya tada bam din.

Haka nan Holland ya gana da shugaban kasar na Iraqi na jeka na-yi ka Fuad Masum, daga bisani ya ziyarci yankin arewacin kasar na kurdawa mai kwariya-kwariyar cin gashin kai har ya gana d a shugabannin yankin.

Shugaban na Faransa ya kuma ziyarci sojopjin kasarsa a Bagadaza, da kuma wadanda suke yankin Kurdistan wadanda suke taimakawa a fafatawar da da ake yi d a 'yan kungiyar ISIS., ya gayawa dakarun cewa kokarinsu yana taimakawa wajen hana akai musu hare-haren ta'addanci a can kjasarsu.288