Shugaban kasar Iran Dakta Hasan Ruhani ne ya bude wannan taron mai taken "Hadin Kai Da Wajibcin Fada Da Kungiyoyin Takfiriyya, Masu Kafirta Musulmi".
A jawabin bude taron, shugaba Ruhani ya bayyana cewar Manzon Allah (s) ya umurce mu da mu tsintsiya madaurinki daya kana kuma mu so juna da nuna halaye na kwarai hatta ga sauran mabiya sauran saukakkun addinai na duniya. Har ila yau shugaban na Iran yayi kakkausar suka ga ayyukan ta'addancin da wasu kungiyoyi suke aikatawa da sunan Musulunci yana mai cewa Musulunci ya barranta da irin wadannan ayyuka na su.
Tsawon kwanaki uku da za a yi ana gudanar da taron, malamai da masana da suka fito daga kimanin kasashen 60 na duniya ne za su gabatar da jawabansu kan muhimmancin hadin kai da kuma hanyoyin da za a bi wajen tabbatar da hadin kai da kuma fada da barazanar da al'ummar musulmi suke fuskanta.
A ranar Asabar ne ake sa ran za a kawo karshen taron inda ake sa ran mahalarta taron za su gana da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei.288