19 Nuwamba 2016 - 16:18
'Yan Ta'adda 950 Ne Suka Rasa Rayukan Su A Kasar Iraki

Shugaban 'yan sandan kasar Iraki Janar Shaker Jodat ya sanar da cewa dakarun kasar Irakin sun sami nasarar kwace dukkanin yankunan kudancin garin Mosul daga hannun 'yan ta'addan Da'esh, inda suka kashe sama da 'yan ta'addan kungiyar su 950.

Kafafen watsa labaran Iraki sun jiyo Janar Jodat yana cewa a jiya juma'a dakarun na su sun sami nasarar kwato murabba'in kilomita 1850 na yankin kudancin Mosul din daga hannun 'yan ta'addan Da'esh kana kuma suka kwato sama da iyalai 10,000.

Har ila yau dakarun kasar Irakin sun tarwatsa motoci 25 da aka makare su da bama-bamai, haka nan da wasu babura 83 su ma da aka makare su da bama-bamai bugu da kari kan wasu makamai daban-daban da aka tarwatsa da kuma kwacewa daga hannun 'yan ta'addan.

Kusan wata guda kenan da dakarun kasar Irakin da suke samun dauki dakarun sa kai na kasar suka kaddamar da yakin kwato garin na Mosul daga hannun 'yan ta'addan.288