2 Nuwamba 2016 - 09:55
An bayar da zabi uku ga 'yan ta'adda a gabashin Halab na kasar Siriya

Ministan harakokin wajen Siriya ya ce 'yan ta'addar gabashin Halab na da zabi uku, ko su meka kansu, ko kuma su bar yankin ko kuma su hallaka.

A yayin da yake amsa tambayoyin 'yan jaridun kasar Burtaniya da suka kai ziyara birnin Damuscus, Walid Mu'alim Ministan harakokin wajen Siriya ya kara da cewa Shugaba Bashar Al-Assad, Al'ummar kasar Siriya ne suka zabe shi, ba shugaban kasar Amurka ko kuma wani mutum na dabanba,  dan haka Al'ummar Siriya na ganin bai dace ba wani Mutum can daban ya bayyana mahangar sa a kan sa ba.

Amurka da kasashen turai gami da na Larabawa bayan kwashe shekaru shida na yunkurin kifar da Gwamnatin Bashar Al-assad ta hanyar amfani da 'yan ta'addar Duniya tare kuma da basu makamai, a halin da ake ciki su na iya kokarin su wajen ganin 'yan ta'adda ba su sha kashi a birnin Halab ko Alepo ba.
Farmakin da Sojojin Siriya tare da samun goyon bayan jiragen yakin kasar Rasha ke kaiwa kan 'yan ta'adda a birnin Alepo na shan suka daga kasashen Amurka da Turai, wanda hakan ke nuna cewa Kasashen Yamman ba da gaske suke ba a yakin da suke ce suna yi da ta'addanci.288