Al-shebab ta kaddamar da jerin hare-haren ne cikin sa’oi 24 a Somalia da kuma kan iyakar Kenya.
Al shebab ta sake kai wani farmakin na daban a wani Otel da ke garin Mandera na Kenya, in da ta kashe mutane 12 kamar yadda maj ‘yan sanda ta sanar.
Al Shebab dai wadda a can baya ta kame wurare da dama a Somalia, na bukatar hanbarar da gwamnatin Mogadishu da ke samun goyon bayan kasashen yammacin duniya.
Sabon harin da kungiyar ta kai, na zuwa ne a dai dai lokacin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben ‘yan majalisar dokokin Somalia, wanda kuma zai kai ga zaben shugaban kasa da zai ci gaba da gina kasar bayan ta yi fama da rikice-rikice na tsawon shekaru.288