13 Agusta 2026 - 18:45
Source: ABNA24
Shekh Zakzaky H: Manzon Allah (S) Shiriya Ne Da Mafita A Kowane Zamani

Da yammacin yau Talata 27 ga watan Safar, 1448 (11/8/2026) ne, Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya rufe Mu'utamar ɗin da Lajanar Maulud da Makon Hadin-kan Musulmi na Harka Islamiyya suka gudanar na kwana biyu a karo na 18 a Abuja. 

A jawabinsa, Shaikh Ibraheem Zakzaky ya bayyana cewa, saƙon Manzon Allah (S) shiriya ne da mafita a kowane zamani. Inda ya ƙara da cewa, abubuwan da suke faruwa a wannan lokacin sun yi kamanceceniya da na lokacin Manzo (S), yayin da siffofin muminai, da na mushrikai da kuma na munafukai suke bayyana a tsakanin mutane. 
Jagora ya bayana cewa, a yau duniya ɓangarori biyu ne: masu biyayya ga Allah da Manzo (S), da kuma Yammacin duniya; wakilan shaiɗan.
Dangane da Mauludin wannan shekarar, Shaikh Zakzaky ya yi kira da a yi amfani da lokutan Mauludi domin kusantar juna da kuma wayar da kan al’umma kan abubuwan da ke faruwa. “Kusancin nan yana kawar da katangar rarrabuwar kai.” Ya jaddada. 
A wani ɓangare na jawabinsa, Jagora ya tunatar tare da jajantawa kan wafatin Manzon Rahma (S) da ya afku a ranar 28 ga Safar, wanda ya ce tunawa da shi da yin jaje raya addini ne. Ya ƙara da cewa, muna tunawa ne don mu ɗauki darasi.


Daga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)
27/Safar/1448
11/08/2026

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha