11 Oktoba 2016 - 19:43
Mahukuntan Iraki Sun Tsaurara Matakan Tsaro A Birnin Karbala Na Kasar Iraki

Kakakin rundunar 'yan sandan kasar Iraki ya bayyana cewa: Sun dauki kwararan matakan tsaro domin kare lafiyar al'umma a yayin juyayin ranakun Tasu'a da Ashura.

Kakakin rundunar 'yan sandan Iraki Hasan Al-Majma'i a yau Talata ya bayyana cewa: Rundunar 'yan sandan Iraki ta hada kai da dakarun sa-kai da nufin kare lafiyar miliyoyin mutane da suka hada da al’ummar Iraki da baki daga sassa daban daban na duniya da suke ci gaba da raya juyayin ranar Tasu’a a garin Karbala a yau Talata.

Kakakin rundunar 'yan sandan ta Iraki ta kara da cewa: Dubban daruruwan mutane ne daga sassa daban daban na duniya suka shiga cikin kasar domin gudanar da juyayin ranar Tasu’a a yau Talata da kuma Ashura a gobe Laraba a garin na Karbala.288