Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S}-abna-Ministan harkokin wajen Pakistan din Khawaj Asif ya ce wata tawagar gwamnati daga kasar wadda zai jagoranta za ta je Saudi din a Talatar nan don tattaunawa kan wannan batu. Gabannin wannan zantawa da kasashen biyu za su yi, ministan tsaron Pakistan din da shugabannin rundunonin tsaro na kasar gami da firaminista Nawaz Sharif sun yi wata ganawa kan tallafawa Saudi din a yakin da ta ke Ansarullah na Yaman . kasar Pakisan dai na daya daga cikin kasashen da ke dasawa da Saudi Arabiya.ABNA
31 Maris 2015 - 11:22
Lambar labari: 680216
Pakistan ta ce za ta tallafawa Saudi Arabia da sauran kasashen yankin Tekun Farisa da ke yakar Ansarullah na kasar Yaman.