6 Janairu 2015 - 12:05
Da'ish sun kashe Irakawa takwas.

Yan ta'adda na gunkiyar Da'ish sun sace mutane da yawa a kudu maso kabashin takrit sannan suka hallaka takwas akan tuhumarasu da yin ridda daga cikin wadanda aka kashen akwai yan sanda.

Kamfanin Dillancin labarai na IRINN ya rawaito yewa wani dan sanda a jahar salahuddin yace; ranar litinin yan ta'adda na kungiyar Da'ish sun sace mutane dayawa wadanda wasu daga cikin su ma'aikata ne da kuma yan gudun hijira ya zuwa yanzu ba a san inda suka kai suba.

Mai bada labarin wanda ya bukaci a sakaya sunann sa yace; kama yanzu yan ta'adda sun kashe mutane takwas daga cikin wadanda suka kama kuma daga cikin su a kwai jami'an yan sanda.

A bage daya, sojojin Iraki da na sa kai na cigaba da samun nasara awurare daban-daban wajan kwato yankunan da suke hannun yan ta'adda.ABNA