Yankin tsauni na Galgala na hannun kungiyar Al Shabaab ne tun tsawon shekaru, inda ya kasance babban sansaninsu a arewacin kasar .
Daga nata waje Kungiyar ta Al Shabaab ta ce ana gwabza kazamin fada a yankin tsakanin mayakanta da hadin gwiwar Sojin kasar da na kasashen Afirka amma dai ta ce har yanzu ita ke da iko da iyakokinta.
A kudancin kasar ta Somaliya ma , hadin gwiwar dakarun tarayyar Afirka da sojojin gwamnatin kasar na ci gaba da dannawa birnin Brava mai gabar teku. ABNA