28 Satumba 2014 - 19:32
Musulman Phillipine Sun Fara Tattauna Batun Ajiye Makamansu Da Gwamnati

Musulmi yan tawaye a kasar Philipine sun fara tattauna batun ajiye makamansu kamar yadda yerjejeniyar sulhu wacce suka cimma da gwamnatin kasar ta bukata a yau Lahadi.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayyana cewa maso shiga tsakanin gwamnatin da yan tawaye musulmi na kudancin kasar Philippine sun fara tattaunawa kan ijiye makaman yan ntawyen a birnin Kwalalampou na kasar Malasia a jiya Asabar kuma tattaunawan zata ci gaba har zuwa ranar litinin.

Wakilai daga kasashen Burunai, Turkia da kuma Nurway na daga cikin wadanda suke shiga tsakani don kawo karshen borin da musulman kasar suka yin a tsawon shekaru kimani 40.

Gwamnatin kasar Philippine ta yi alkawarin bawa musulman kasar kwarya kwayan yencin kai a yankin da suka fi yawa na kudancin kasar don kawo karshen tawayen da suke yi fiye da shekaru 40 da suka gabata. ABNA