A ganawarsa da manema labarai a gefen zaman taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya karo na 69 da ake gudanarwa a birnin New York na kasar Amurka a yau Asabar; Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrof ya bayyana cewar kasar Amurka domin cimma manufofinta a duniya ta dauki matakan tsoma baki a harkokin kasashen duniya da dama, kuma ya bayyana a fili cewa kasar ta Amurka tasha kashi a kasashen Afganistan, Iraki da Libiya.
Lavrof ya kara da cewar a halin yanzu haka kasar ta Amurka tana ta kokarin ganin bayan gwamnatin Bashar Asad a kasar Siriya amma yau tsawon shekaru fiye da uku ta kasa cimma nasara.
Ministan harkokin wajen kasar ta Rasha ya kara da cewar Amurka da kawayenta na yammacin Turai sun dauki kansu a matsayin mafiya tsarkin al’umma tare da karfin wanzar da doka, don haka suke kokarin ganin sun juya akalar kasashe yadda suke so. ABNA