21 Satumba 2014 - 09:07
Palasdinuwa Da HKI Zasu Dawo Kan Teburin Tattaunawa Ranar Laraba

Jami’an gwamnatin kasar Masar da kuma tokororinsu na Palasdinu sun bada sanarwan cewa a ranar laraban mai zuwa ce za’a sake farfado da tattaunawa (ba ta kai tsaye ba) tsakanin Palasdinawa da kuma HKI.

A ranar 26 ga watan Augustan da ta bagata ce bangarorin HKI da kuma kungiyoyi masu gwagwarmaya a yankin Gaza suka cimma yejejeniya ta tsagaita bude wuta bayan yaki na kwanaki 51.

Yerjejeniyar tsagaita bude wutan dai ta bukaci bangarorin biyu su sake dawowa kan teburin tattaunawa bayan wata guda da tsagaita bude wuta don ci gaba da tattaunawa kan batutuwan da ba’a kamala tattauwana a kansu ba.

Batutuwan da za’su tattauna a wannan karon dai sun hada da bude tashan jiragen ruwa da kuma tashar jiragen sama a yankin gaza.

Har’ila yau za su tattauna batun fursinonin yakin wadanda suke tsare a gidajen yarin HKI da kuma yadda za’a yi musayarsu da gawakin sojojin yahudawa wadanda suke tsare a hannun dakaru masu gwagwarmaya a yankin na gaza.