Rahotonni daga Benghazi na kasar Libiya sun bayyana cewa: Wasu ‘yan bindiga dadi sun bude wuta kan Ahmad Habib Masmari tsohon hafsan sojin sama a kasar Libiya, inda suka same shi a kansa, kuma hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsa nan take a garin Benghazi da ke gabashin Libiya.
Har ila yau wasu gungun ‘yan bindiga sun kai farmaki kan bankin Ijma’ul-Arabi da ke tsakiyar garin Benghazi a safiyar yau Alhamis, inda suka yashe bankin ta hanyar kwashe kudade dinari miliyan daya da dubu dari bakwai, daidai da dalar Amurka miliyan daya da dubu dari uku da tamani. ABNA