Hujjatul Islam wal muslimin Kazim Siddiqi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da hudubar sallar Juma’a a yau din nan Juma’a inda ya bayyana wannan nasarar a matsayin wata mu’ujiza ta tafarkin gwagwarmaya yana mai cewa babu wani abin da HKI ta samu a yakin in ban da shan kunya da kuma karin kyama a zukatan al’ummomin duniya.
Yayin da ya koma kan abin da ke faruwa a kasar Iraki kuwa, na’ibin limamin Juma’ar na Tehran ya yi fatan al’ummar kasar za su hada kansu waje guda wajen tinkarar wannan makirci da aka kulla musu.
Har ila yau Hujjatul Islam Siddiqi ya taya gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta Iran murnar zagayowar makon gwamnati da ake ci gaba da gudanarwa a nan Iran yana mai jinjinawa wa matsayar da gwamnatin ta dauka kan batutuwan da suke faruwa a yankin gabas ta tsakiya da ma duniya musamman kan irin kokarin babakeren Amurka bisa jagoranci da shiryarwar Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei. ABNA