A wata ganawa da ya yi cikin dare, a New York, kwamitin ya amince da wani kudiri, da ke bukatar Israela da Hamas da su yi kokarin cimma yarjejeniya mai dorewa ta tsagaita wuta, da za ta bayar da dama a kai kayan agaji ga fararen hula da fadan ya rutsa da su.
A jiya Lahadi, bangarorin biyu sun kara kaimi wajen kai hare-hare, inda kowanne ke zargin dayan da saba yarjejeniyar wucin gadi ta tsagaita wuta.
Jakadan diflomasiyya na Palasdinawa a Birtaniya, Manuel Hassassian, ya gaya wa BBC cewa, Hamas a shirye take ta amince da shawarar dakatar da bude wuta
Ya ce, '' Idan Isreala ta dakatar da kai hare-hare ta sama da kisan kan mai-uwa-da-wabi, ina ganin Hamas za ta saka hakan.' ABNA