A jawabin da ya gabatar dazun nan, shugaban kasar ta Syria, ya ce; Bayan gushewar shekaru uku da rabi, al’ummar kasar Syria sun aiwatar da abinda su ka kudurce.: Shugaba Asad ya ce; zaben da aka yi yan a a matsayin kuri’ar raba gardama ce ta fada da ayyukan ta’addanci da kuma rusa manufofin manyan kasashe. Da ya koma magana akan kasashen da su ke taimakawa ‘yan ta’adda, shugaba Asad ya ce; Kasashen da su ke taimakawa ayyukan ta’addanci za su dandana kudarsu. Haka nan kuma ya yi suka da kakkausar murya akan Pira ministan kasar Turkiya Rajab Tayyib Urdugan. Dangane da Saudiyya kuwa, shugaba Asad ya soke da cewa manufarta ita ce mika kai da rusunawa ga makiya. Dangane da abinda yak e faruwa a Palasdinu kuwa, shugaba Basshar Assad ya batun Palasdinu zai ci gaba da zama mafi muhimmaci ga kasarsa, haka nan kuma ya ce; duk abubuwan da su ke faruwa a cikin wannan yankin na gabas ta tsakiya yana da alaka ne da Palasdinu.ABNA
16 Yuli 2014 - 13:21
Lambar labari: 624465
Shugaban Kasar Syria Basshar Asad ya yi rantsuwar kama aiki bayan da ya lashe zaben shugabancin kasar a karo na uku