Sakataren tsohon firayi minista Sadiq al-Mahdin Muhammad Zaki ya shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP cewa a daren jiya asabar ne wasu gungun jami’an tsaron kasar suka suka zo gidan Sadiq al-Mahdi da takardar sammaci inda suka tafi da shi.
Wata majiyar gwamnatin ta Sudan dai ta shaida wa kamfanin dillancin labaran na AFP cewa ana tsare da Al-Mahdi ne bisa umurnin babban mai shigar da kara na kasar saboda ci gaba da yada irin wannan zargi da dakarun na fada da masu tada kayar bayan.
Kame Al-Mahdin ya biyo bayan wani jawabi ne da ya yi a safiyar jiya asabar din a jihar Gezira da ke kudancin birnin Khartoum, fadar mulkin kasar ta Sudan inda ya ce wajibi ne a kawo karshen take hakkokin bil’adama da jami’an tsaron kasar suke yi da kuma sake jaddada wannan zargin.ABNA.