Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya ce shugaba Catherine Samba Panzan ta yi wannan kiran ne a wata ganawa da ta yi da wakilan kungiyoyi masu zaman kansu na kasar inda ta ce wajibi ne a dau matakan da suka dace wajen kare musulmin da suke babban birnin don kiyaye yanayin zamantakewa da samuwar mabiya addinai daban daban a babban birnin.
Shugabar ta kara da cewa a halin yanzu dai sama da kashi 90 cikin dari na musulmin da suke birnin na Bangui sun gudu daga birnin sakamakon hare-haren da ake kai musu, don haka ta ce wajibi ne a dau matakan da suka dace wajen kiyaye wadanda suka sauran.
Musulman da ke zaune a birnin na Bangui suna ci gaba da gudu ne sakamakon kisan gillan da ‘yan kungiyar Anti-Balaka suke ci gaba da yi musu ne da kuma gazawar da sojojin Faransa da na Tarayyar Afirka suka nuna wajen kare musu lafiyarsu.ABNA.