Wani shaida a wurin ya fadawa BBC cewa, bam din ya halaka mutane da dama kuma ana ci gaba da kwashe gawarwakin mutane da kuma wadanda bam din ya jikkata.
Yanzu haka dai jami'an tsaro sun garzaya wurin, kuma motocin hukumar bada agajin gaggawa suna ci gaba da kwashe mutanen da suka jikkata.
Mazauna unguwar suna cewa, abinda ya fashe din ya girgiza gidajen unguwar, kuma mutane sun kidime sosai.ABNA.