Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) - ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Ayatullah Ramezani, Babban Sakataren Majalisar Duniya ta Ahlul-Bayt (AS), a Maukibin masoya Imam Hussain (Maukibin Mutanen Afirka), Tanti mai lamba 375, ya yi bayani game da dangantakar tarihi, siyasa, da akida tsakanin nahiyar Afirka da makarantar farkawa ta Imam Shahidin Al'umma da kuma yuunkurin Ashura.
Bilalul-Habashi; Mu'ujizar Daidaito Da Juriya A Kan Azabtarwa
Ya bayyana cewa dubin Majalisar Duniya ta Ahlul-Bayt (AS) ga nahiyar Afirka ba dubi ne na kayan aiki ba, sai dai dubi ne a matsayin "dama" mai girma, kuma ya nuna cewa wannan dangantaka tana da tushe a farkon Musulunci da kuma dabi'ar halittar mutanen wannan nahiya.
Babban Sakataren Majalisar Duniya ta Ahlul-Bayt (AS), yayin da yake nuni ga mutuntakar Bilalul-Habashi a matsayin wakili na farko na mutanen Afirka a gaban Annabi (SAW), ya bayyana cewa Bilal, sabanin mutane da yawa waɗanda suke neman mu'ujiza don su yi imani, shi bai nemi wata mu'ujiza ba; domin a gare shi, maganar Annabi ta annabta da bata bambanta tsakanin Balarabe da wanda Balarabe ba, baƙi da fari, ita ce mafi girman mu'ujiza a gareshi.
Ya kara da cewa Bilal a kan wannan imani na ɗan'adam, ya jimre mafi tsananin azabtarwa, kuma bai yarda ya bar aqidarsa ta zuciya ba.
Ta’addancin Mulkin Mallaka A "Gidan Bayi" Ya Dauki Shekaru 300 Tare Da Wawashe Ma'adinai
Ayatullah Ramezani ya ci gaba da yin nuni ga tsare-tsare masu rikitarwa na mulkin mallaka don rage ci gaban Afirka, ya kuma ambaci ƙasashen Faransa, Ingila, da gwamnatin Isra’ila a matsayin manyan masu laifin mulkin mallaka na zamani.
Ya nakalto abubuwan da ya gani da idonsa a tsibirin "Gorée" a Senegal da "Gidan Bayi," ya bayyana cewa masu mulkin mallaka na tsawon shekaru 300 suna bautar da mutane masu tsaftar halitta, kuma ta hanyar raba iyalai da zalunci, suna sayar da uba, uwa, da 'ya'ya zuwa ƙasashe daban-daban.
Ya bayyana cewa Afirka tana ɗaya daga cikin wurare mafi arziki a duniya ta fuskar albarkatun ƙasa da duwatsu masu daraja, kuma ya ce Turawa ta hanyar tallace-tallace marasa kyau da tsoratarwa, sun yi ƙoƙarin hana wasu tafiya zuwa wannan nahiya don su wawashe dukiyoyinta masu yawa cikin kwanciyar hankali.
Canjin Ma'aunin Ƙarfi; Barazanar Soji Na Maƙiyi A Nisan Kilomita 5,000
Babban Sakataren Majalisar Duniya ta Ahlul-Bayt (AS), a wani ɓangare na jawabinsa, ya yi magana game da manyan canje-canje bayan juyin juya halin Musulunci, kuma ya bayyana cewa a yau matasan Afirka, ta hanyar koyi da darasin "Za mu iya" na Imam, sun sake gano ainihin asalinsu, kuma ya nanata wajabcin sanin maƙiyi. Yayin da yake nuni ga raba kan 'yan Shi'a da 'yan Sunna da kuma kashe Musulmai a yankuna kamar Myanmar, ya bayyana cewa maƙiya koyaushe suna neman kunna wutar rashin jituwa tsakanin Musulmai.
Ayatullah Ramezani, yayin da yake kwatanta lokacin rauni na baya da ƙarfin ginshikin juriya na yau, ya nuna cewa a da ana harbo mana jirginmu kuma ba mu da ikon mayar da martani, amma a yau ma'auni ya canza; a yau idan suka harbo ɗaya, za su yi asarar biyu; har ma da Ingila wacce ke da nisan kilomita 5,000 daga gare mu, an aika da sako cewa idan wani jirgin sama ya tashi a kanmu, za mu harbo shi a can.
Arba'in Da Bayyanar Makarantar Imam Shahidi; Daga Girman Jana'iza Zuwa Ruwayar Zainab As
Ya nanata cewa Imam Shahidi ya tarbiyyantar da al'ummar da a yau ke tsaye a gaban "masu wawashe dukiyoyin duniya," kuma ya bayyana cewa taken "Haihata Minnal-Zilla" da muka koya a Karbala, a yau wannan al'umma ta aiwatar da shi a fagen al'umma.
Ayatullah Ramezani, yayin da yake tunawa da jana'izar mutane miliyan 11 na gawar Imam Shahidi da sallar da aka yi masa cikin sufanci na Allamah Jawadi Amuli a Masallacin Jamkaran, ya bayyana shi a matsayin wanda aka zalunta mai iko, wanda hotonsa a duk hanyar Arba'in ke ƙarfafa mahalarta ziyara.
A ƙarshe, yayin da yake yabon karimcin da ba a misaltuwa na al'ummar Iraqi da kwatanta shi da wahalhalun ayarin fursunonin Karbala, ya bayyana kasancewar matasan Afirka masu ilimi a Iran a matsayin dama don isar da sakon farkawa zuwa nahiyar Afirka, kuma ya bayyana cewa wannan yunkurin, da ikon Allah, zai haɗu da yunkurin duniya na Imam Mahdi (AS).
……..
Ra'ayinka