Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) - ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Tun da aka isa masaukin, an gudanar da shirye-shiryen hutawa, sallar jam'i, da rabon abinci da ruwa ga masu tattaki. Haka kuma masu hidima sun ci gaba da gudanar da ayyukansu domin tabbatar da jin daɗin masu attakin.
An gudanar da tattakin cikin kwanciyar hankali, tare da nuna juriya, haɗin kai da taimakon juna tsakanin mahalarta. Insha Allah za a ci gaba da tafiya da safe, idan Allah Ya kaimu domin ci gaba da wannan tafiya ta Yaumul Arba'een.
Alhamis 30/7/2026
Rahoto: SK PRESS TV
Hoto: Badaru Rabi'u Mai Sufi
Ra'ayinka