Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) - ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Hizbullah ta Lebanon ta bayyana cewa sojojin Isra'ila na ci gaba da lalata da rushe ababen more rayuwa da abubuwan da ake buƙata na rayuwa a kudancin Lebanon, don hana mazauna waɗannan yankuna komawa ƙauyukansu.
Sashen hulɗa da jama'a na Hizbullah a cikin wata sanarwa, ta dora alhakin ci gaba da "laifukan gwamnatin Isra’ila" ta hadin gwiwar gwamnatin Lebanon.
Hizbullah ta kuma buƙaci gwamnatin Lebanon ta daina rashin nuna halin ki in kula da buƙatun jama'a.
A cikin wannan sanarwa ya zo: Idan gwamnatin Lebanon ba ta da ikon gudanar da ayyukanta, aƙalla kada ta hana mutane yin amfani da halastaccen haƙƙinsu don kare rayukansu, ƙasarsu, da haƙƙoƙinsu.
Hizbullah ta kuma buƙaci gwamnatin Lebanon ta gudanar da ayyukanta na ƙasa da na tsarin mulki, kuma ta ɗauki mataki don dakatar da ayyukan rusau da Isra'ila ke yi.
Wannan ƙungiya a ƙarshe ta buƙaci al'ummar duniya da su ɗauki nauyin da ke kansu, kuma su tilasta wa Isra'ila dakatar da hare-hare da ficewa daga dukkan yankunan da ta mamaye na Lebanon.
Ko da yake Lebanon da gwamnatin Isra’ila a baya sun sanya hannu kan "Yarjejeniyar Tsari" ta hanyar shiga tsakani na Amurka, amma hare-hare da keta tsagaita wuta daga Tel Aviv na ci gaba.
A lokaci guda, wannan yarjejeniya ta fuskanci suka, kuma masu suka sun yi nuni ga rashin fayyace matsayin shari'a na yarjejeniyar da kuma rashin tsarin lokaci na ficewar sojojin Isra’ila.
………………
Ra'ayinka