21 Yuli 2026 - 18:24
Source: ABNA24
Cikakkun Bayanai Hare-haren Amurka A A Jiya Da Safiyar Yau Kan Wurare Hudu A Sassan Iran

Da safiyar Talata, a ci gaba da hare-haren sama na makiya Amurka a kan larduna daban-daban na ƙasar, sun harba wani rokar yaƙi kan ɗaya daga cikin tsaunukan birnin Shiraz.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) - ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Da safiyar Talata, a ci gaba da hare-haren sama na makiya Amurka a kan larduna daban-daban na ƙasar, an harba wani makamin rokar yaƙi kan ɗaya daga cikin tsaunukan birnin Shiraz. An jiyo karar wannan saukar wanna bom din a wasu wurare na Shiraz.

Za a bayyana cikakken bayani game da wannan lamari da girman barnar da aka samu nan gaba.

Sannan Mataimakin gwamnan Fars kan harkokin siyasa, tsaro da zamantakewa ya ba da rahoton nasarar sojojin da ke wannan lardin wajen harbo wani harin jirgin maras matuki na Amurka a tsaunukan garin Dezhkard, na gundumar Saddeh na Eqlid.

Mataimakin gwamnan Fars, yana mai nuni da cewa an yi wannan mataki ne a cikin sa ido na yau da kullun akan motsin makiya, ya jaddada cewa: Duk wani ta'addanci da rashin tsaro a lardin Fars, za a fuskan ce shi da martani mai ƙarfi da gaggawa daga sojoji.

Cikakkun Bayanai Hare-haren Amurka A A Jiya Da Safiyar Yau Kan Wurare Hudu A Sassan Iran

Sannan Gwamnan Abdanan ya ce: Makiya Amurka masu ta'addanci sun kai hari a wasu yankuna na kewayen birnin Abdanan da makamai masu linzami da yawa.

Behzad Noormohammadi a cikin wata hira ya bayyana cewa: Makiya da safiyar yau Talata 21 ga Yuli, ta hanyar harba makamai masu linzami guda 2, sun kai hari a wasu yankuna a wajen birnin Abdanan da kuma a tsaunukan Dinar Kuh, kuma a wannan harin ba mu sami asarar rayuka ko dukiya ba.

Ya yayi ishara da cewa: Ma'aikatan agaji suna jibge a yankin, kuma suna nazarin fannonin lamarin.

Cikakkun Bayanai Hare-haren Amurka A A Jiya Da Safiyar Yau Kan Wurare Hudu A Sassan Iran

Haka ma Gwamnan Neyriz ya ba da rahoton nasarar aiwatar da aikin kakkabo wani jirgin makami mai linzami na cruise na makiya Amurka a sashen Qatruyeh na wannan gundumar.

Ya kara da cewa: Nan da nan bayan faduwar jirgin mai dauke da makamin, rundunonin soji sun isa wurin, kuma an kammala aikin tabbatar da tsaro da kawar da wannan jirgin makami jiya 20 ga Yuli, ta sojojin tsaro cikin nasara.

Gwamnan Neyriz, game da wurin da jirgin makamin ya fado, ya bayyana cewa: Wurin da jirgin makamin ya fado yana cikin filayen noma, kuma an yi sa'a cewa ba ya kusa da wuraren zama, cibiyoyin masana'antu ko wuraren soji.

Cikakkun Bayanai Hare-haren Amurka A A Jiya Da Safiyar Yau Kan Wurare Hudu A Sassan Iran

A ƙarshe ya jaddada cewa: A yayin wannan aiki, babu wani fashewa da ta faru, kuma an tabbatar da tsaro da kawar da jirgin makamin gaba ɗaya.

………

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha