Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) - ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Dakarun Juyin Musulunci na Iran, tare da fitar da wata sanarwa, sun sanar da cewa jiragen ruwan dakon mai guda biyu masu keta doka, da nufin wucewa ta wata hanya a kudancin mashigar Hurmuz, sun fuskanci wata babbar gobara sakamakon kai masu hari, kuma an dakatar da su.
Sa'o'i da suka gabata, jiragen ruwan dakon mai guda biyu masu keta doka, waɗanda da yaudarar sojojin Amurka masu kashe yara suke nufin wucewa ta hanyar haɗari a kudancin mashigar Hurmuz, sun fuskanci wani bban ahri da ya haifar masu da babbar gobara, tare da dakatar da su. Rundunonin agaji da ceto suna fitar da ma'aikatan waɗannan jiragen ruwa daga yankin.
Rundunar ruwa ta dakarun juyin musulunci ta sake yin gargadi ga kamfanonin jigilar kayayyaki, su kula da lafiyar ma'aikatansu da jiragen ruwansu, kuma kada su amince da bayanan karya na sojojin Amurka, kuma su guji hanyoyin da ba su da tsaro da haɗari.
A bayyane yake cewa, matuƙar munanan ayyukan Amurka suka ci gaba a yankin, mashigar Hurmuz a rufe take, kuma ba za a fitar da ko digo ɗaya na man fetur da iskar gas ko kwandon takin mai guba daga yankin ba.
An fara aikin hukunta sansanonin Amurka masu ta'addanci, saboda laifukan ruwa, kuma za a kawo rahotonsa gare ku.
Kuma Babu Wata Nasara Fa Ce Daga Wurin Allah Mabuwayi Mai Hikima.
………………….
Ra'ayinka