Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) - ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Jaridar Wall Street Journal a cikin wani rahoto, ta nakalto daga jami'an Amurka, ta ba da rahoton daidaituwar ƙarfin soji na Iran da tsarin tsaron Amurka.
Rundunar Sojojin Amurka (CENTCOM) ta sanar jiya cewa sojojin Amurka biyu sun mutu a harin Iran na shekaranjiya a Jordan, kuma wani soja ya bace. Wannan ita ce asarar farko da sojojin Amurka suka sanar tun bayan sake faruwar rikici da Iran.
Jami'an Amurka sun shaida wa jaridar New York Times cewa sojojin Amurka da dama sun jikkata a Jordan a kwanakin baya.
Baya ga asarar rayuka, hotunan tauraron dan adam sun tabbatar da cewa, biyo bayan harin Iran a kan sansanin Amurka a Jordan, an lalata rumfunan shirya jiragen yaƙi.
Jaridar Wall Street Journal a cikin wani rahoto ta sanar da cewa an kashe sojojin Amurka a sansanin sojan sama na Muwaffaq al-Salti; wannan sansanin da tsarin tsaron makamai masu linzami na TAD na Amurka ke girke ya fuskanci harin Iran a watan Maris.
Jami'an Amurka masu Saniya akai sun shaida wa Wall Street Journal cewa Iran ta daidaita makamanta da tsarin tsaron Amurka, kuma tana amfani da makamai masu linzami masu sauri waɗanda suke da ƙarfin motsi lokacin da suke kusantar ƙasa.
Dangane da wannan rahoto, ikon Iran na kai hari a kan manufofi masu muhimmanci, ya haifar da damuwa tsakanin jami'an Amurka.
A cewar kafar yada labarai ta yahudawa Ynet, a daidai lokacin da waɗannan abubuwan ke faruwa, rahotanni a Amurka sun nuna cewa Pentagon tana nazarin darussan yaƙin da ake yi da Iran.
………………
Ra'ayinka