Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA – ya bayar da rahoton cewa: A cikin nazarin kafofin yada labaran Amurka game da abubuwan da suka faru na baya-bayan nan a yaƙin yanki da hare-haren da Iran ta kai a matsayin martani ga keta tsagaita wuta da Amurka ta yi a kan wuraren da take da su a yankin, Mujallar Atlantic a cikin wani nazari mai taken "Ikon Yaƙi Yana Hannun Iran Kuma Trump Ya Cika Da Rudani Kuma Ya Nutsa Cikin Matsaloli Kuma An Wulakanta Shi," ta rubuta: Ikon yaƙin da ke tsakanin Amurka da Iran a yanzu yana hannun tsarin Iran ne, ba Donald Trump ba, kuma fahimtar juna da aka kulla kwanan nan, hasashe ne kawai da Trump ya kwallafa rai da shi, Iraniyawa sun wulakanta shi sau da yawa.
Wannan kafar yaɗa labarai ta Amurka ta jaddada cewa Trump ya yi tunanin cewa yana da iko a kan yaƙin da ya tsokano, amma gaskiyar ita ce, ya rasa ikonsa, kuma Iraniyawa ne ke kayyade yanayin yakin, kuma sun wulakanta shi sau da yawa. Bugu da kari, tsagaita wuta da Trump ya ayyana a watan da ya gabata, wanda mai yiwuwa don kwantar da kasuwannin duniya da kuma hana duk wani mataki na shari'a daga majalisar Amruka a kan Trump, ba ta da tasiri; domin babu wani bangare da ya dakatar da wutar.
A ci gaban wannan makala an ce: Halin da ake ciki yanzu ya zama wani abu kamar yaƙi sannu a hankali, kuma a cikin kwanakin da suka gabata Iraniyawa sun kai hari a kan jiragen ruwan dakon mai guda uku a mashigar Hurmuz, kuma Amurkawa ma sun kai hari a kusan wurare 80 a Iran. Kwanan nan ma, dakarun juyin musulunci na Iran sun sanar da cewa sun kai hari a kusan wurare 85 na Amurka a Bahrain da Kuwait.
Bisa ga wannan rahoto, a ranar Alhamis an tambayi Trump ko yarjejeniyar fahimtar juna da Iran, wadda aka tsara ta zama tushen tattaunawa, ta ƙare ko a'a, ya ɗan yi shiru, sannan ya ce: "Wannan tambaya ce mai ban sha'awa, ni a iya sanina ina ganin tsagaita wuta ta ƙare, kuma ba na son yin hulɗa da Iraniyawa."
Atlantic ta jaddada cewa: Yarjejeniyar fahimtar juna da aka kulla tsakanin Tehran da Washington takarda ce ta mika wuyar Amurka da Iraniyawa suka tilasta, kuma Trump yana son ficewa daga yaƙi don haka ya sanya hannu. Manufofin Iran a wannan yarjejeniya sune: wanzuwar tsarin, ikon sarrafa mashigar Hurmuz, da kuma kiyaye shirin nukiliya.
Trump Na Shure-Shure Cikin Rikici Da Yaƙi
A ci gaban wannan rahoto an jaddada cewa gwamnatin Trump ta shiga wannan yaƙi a makance ba tare da dabara a fili ba, kuma ta dogara da zato marasa cika, tsoffin bayanai da hasashe. Jami'an Amurka ma, a ƙarƙashin tasirin rudanin Trump, sun yi tunanin cewa tsarin Iran zai rushe da sauri.
Bisa ga wannan rahoto, Trump da Pete Hegseth, ministan yakinsa, sun yi watsi da nazari da shirye-shiryen soji da leken asiri na shekaru da yawa, sannan lokacin da Iraniyawa suka rufe mashigar Hurmuz kuma suka shaƙe tattalin arzikin duniya, gaba ɗaya suka yi mamaki, kuma tun daga wannan lokacin manufar gwamnatin Amurka ta zama magance rikicin mashigar Hurmuz. Yaƙi ta hanyar bama-bamai ba tare da ikon sarrafa yanki ba, ba shi da amfani, kuma Amurka tana asarar yawan kayan yakinta masu tsada ba tare da samun nasarorin dabaru ba.
Mujallar Atlantic a ƙarshe ta jaddada cewa maganganun Trump ba su nuna shugaba mai jagorantar yaƙi ba ne; sai dai, suna nuna mutum mai cike rauni wanda ya fada cikin matsalolin da suka wuce ƙarfinsa, kuma maimakon ya sarrafa abubuwan da ke faruwa, yana ba da martani na gaggawa kawai.
Jaridar Amurka New York Times ita ma a ranar Alhamis a wannan fanni ta sanar da cewa: Trump yanzu yana fuskantar sakamakon yarjejeniyar da aka tsara cikin gaggawa don ba shi damar da'awar nasara ta siyasa; duk da cewa batutuwa masu muhimmanci sun ci gaba da kasancewa ba a warware su ba, ciki har da shirin nukiliya na Iran, tarin makamanta masu linzami, taka rawar yanki na Tehran da tsaron zirga-zirgar ruwa a mashigar Hurmuz.
Wannan kafar yaɗa labarai ta Amurka ta ba da rahoton cewa Trump ya tafka caca mai girma, kuma ya yi tunanin cewa jagorancin Iran zai canza halinsa saboda muradun tattalin arziki, amma ya gane cewa tunanin da ya kasance tun daga 1979, wato kafuwar juyin juya halin Musulunci na Iran, har yanzu yana kan wannan ƙasa.
Bisa ga wannan rahoto, tare da rugujewar tsagaita wuta, Trump ya sami kansa yana fuskantar zaɓuɓɓuka uku masu sarkakiya, duk suna da tsada:
1. Ƙaruwar aikin soji mai faɗi wanda zai iya jawo Amurka cikin sabon yaƙi wanda ba shi da goyon bayan cikin gida.
2. Sake aiwatar da killacewar tattalin arziki da Teku na dogon lokaci a kan Iran wanda ke buƙatar kasancewar soji mai yawa na Amurka.
3. Karɓar wanzuwa cikin halin ba yaƙi ba zaman lafiya wanda ke tattare da lokuta na hare-hare da tattaunawa.
Waɗannan nazarin na Amurka gaba ɗaya sun kai ga wannan sakamakon cewa rugujewar tsagaita wuta ba wai kawai ya sanya Trump a cikin zaɓuɓɓuka masu wuya ba ne, a'a, sai dai yana nuna gazawar dogaron da aka yi kan wata yarjejeniya ta wucin gadi wadda ba ta magance tushen rikicin ba. Haka kuma yayin da Washington ke neman hana yaƙi gaba ɗaya, da alama Tehran ta shirya don arangama mai tsawo inda take haɗa lissafin soji da matsin tattalin arziki da haƙƙoƙin siyasa na bangarorin biyu da ke rikici.
.......................
Your Comment