Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya bayar da rahoton cewa: Babban Laftanar matukin jirgi Ali Abdullahi, kwamandan hedikwatar Khatamul-Anbiya (S.A.W), a cikin wani sako da ya rubuta: Tare da mika ta'aziyya da juyayi a munasabar shahadar jagoran Musulmai da masu 'yanci na duniya, Ayatullahil-Uzma Imam Khamene'i (Allah Ya tsarkake ruhinsa mai tsarki), ga mai wannan zamani (raina da ranmu su zama fansa gare shi), jagora mai hikima na juyin juya hali, Ayatullahil-Uzma Imam Sayyid Mujtaba Husaini Khamene'i (Allah Ya tsare shi) da kuma al'ummar Musulunci; a kwanakin da suka gabata, duniya ta shaida ƙirƙirar wani abin tarihi da ba a taɓa yin irinsa ba da zai dawwama a tarihi.
A ci gaban wannan sako yazo cewa: Jana'izar da rakiyar Imam Shahidin al'umma, a matsayin alama da nuni na girma, basira, imani, jihadi da tsayin daka, da ya rubutu ya tabbatu a ƙwaƙwalwar bil'adama.
A cikin sakon kwamandan hedikwatar Khatamul-Anbiya (S.A.W) ya zo: Ni, tare da girmama darajar wannan jagora shahidi mai girma, na ɗauka a kan kaina wajibi ne in bayyana godiya da girmamawata ga al'ummar Iran da ba a taɓa yin irinsu ba, masu daraja da girma, da kuma Al'ummar Iraki masu kishi, jami'ai da sojojin ƙasar 'yan'uwa da abokai, mayaƙan Musulunci da dukkan Musulmai da masu 'yanci na duniya waɗanda da kasancewarsu na musamman mai ma'ana a ayyukan bankwana da rakiyar shugaban shahidai na juyin juya halin Musulunci da gaban tsayin daka, suka haifar da wani abin tarihi mai girma.
Babban Laftanar Abdullahi a cikin sakonsa ya kawo cewa: Halartar al'ummar Musulunci da ba a taɓa yin irinsa ba, fiye da taron bankwana, da shelanta neman gaskiya ne mai ƙarfi da kuma sake zana layi akan makircin masu girman kai na duniya, wanda ya bambance gaskiya da ƙarya a fili. Wannan yunkurin ɗan adam, alama ce ta haɗin kai mai zurfi tsakanin azamar al'ummomi masu farkawa da hanyar shahada mai ɗaukaka.
A ci gaban wannan sako yazo cewa: Duniya da shugabannin kafirci da girman kai na duniya, musamman Amurka mai laifi da gwamnatin yahudawa, kada su ɗauki baƙin cikin da ke cikin idanun al'umma da kuma kukan da ke fitowa daga wannan baƙin ciki a matsayin rauni.
Kwamandan hedikwatar Khatamul-Anbiya a cikin sakonsa ya jaddada cewa: Wannan baƙin ciki da fushi mai tsarki, zai ci gaba a kan hanyar neman fansar jini kan masu kisan jagora shahidi da shugaban Musulmai da masu 'yanci na duniya da shahidan da ake zalunta na yaƙe-yaƙe na biyu da na uku, kuma zai kai su ga sakamakon ayyukansu.
Babban Laftanar Abdullahi a cikin sakonsa ya kawo cewa: 'Ya'yan al'umma masu jarumtaka a cikin sojoji, tare da dogaro da taimakon Allah Maɗaukaki da goyon bayan al'ummomin Musulmai da masu neman 'yanci, da yunkurin juyin juya hali, za su hana makiya barci, kuma za su yi ramuwa kan masu aikata waɗannan laifukan ta'addanci ko ba dade ko ba jima.
......................
Your Comment