9 Yuli 2026 - 00:49
Source: ABNA24
An Ji Karar Fashe-fashe Da Dama Bandar Abbas, Chabahar, Sirik da Konarak Da Bushehr

An Ji Karar Fashe-fashe a Bandar Abbas, Chabahar, Sirik da Konarak da Bushehr 'Yan mintuna da suka wuce

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA – ya ruwaito cewa: Tun daga yammacin yau Laraba wasu majiyoyin labarai sun ba da rahoton jin karar fashe-fashe da dama a garuruwan Bandar Abbas da Sirik a lardin Hormozgan sannan da aukuwar wasu fashe-fashen a birnin Bushehr a yanzu yanzu

Har ila yau, wannan kamfanin dillancin labarai ya rubuta: 'Yan mintuna da suka wuce an ji karar fashe-fashe da dama a Chabahar da Konarak. Har yanzu babu wani bayani game da yanayin waɗannan kararraki ko kuma yiwuwar asarar rayuka da dukiyoyi.

Babu wani jami'i na hukuma da ya yi tsokaci kan wannan batu.

'Yan mintuna da suka wuce mutane a Chabahar da Konarak su ma sun ji karar fashe-fashe da dama.

Dangane da rahotannin jama'a, har zuwa yanzu an ji karar fashe-fashe kusan 15 a Chabahar da Konarak.

An kuma samu katsewar wutar lantarki a wani yanki na garin Chabahar.

Dangane da wasu labaran da ba na hukuma ba, sansanin Imam Ali (NDSA) a Chabahar ma a daren yau an kai masa hari da jiragen yaki na Amurka.

Har ila yau, Amurka ta kai hari kan garin Chabahar da ke bakin teku da makamai masu linzami da dama, wanda ya haifar da lalata tashar loda kaya ta Shahid Beheshti da ofishin ƴan sanda da hasumiyar kula da harkokin ruwa.

Shugaban kamfanin rarraba wutar lantarki na lardin Sistan da Baluchistan ya kuma sanar da cewa: Sa'o'i da suka wuce sakamakon harin makiya, an katse layukan wutar lantarki guda uku a gundumar Chabahar, kuma da ƙoƙarin ma'aikata an dawo da layuka biyu, yayin da layin na uku kuma za a dawo da shi nan ba da jimawa ba.

Cibiyar Kwamandan Sojojin Amurka ta Tsakiya (CENTCOM) a yau Laraba da yammacin rana ta sanar da cewa sojojinta, bisa umarnin Donald Trump shugaban Amurka, sun fara sabbin hare-hare kan wasu hadafofi a Iran.

CENTCOM ta yi iƙirarin cewa: Manufar waɗannan hare-haren ita ce ƙara rage ƙarfin Iran na yin barazana ga 'yancin zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar Hormuz.

..........

Your Comment

You are replying to: .
captcha