Majiyoyin Republican sun gabatar da sunan gwamnan jihar Florida Ron DeSantis a matsayin yiwuwar maye gurbin Hegseth. DeSantis mai shekaru 48, wanda a baya ya kasance hafsan shari'a a sojin ruwan Amurka, kuma an tura shi lardin Al-Anbar a shekarar 2007, inda ya ba da tallafin shari'a ga ayyukan sojojin musamman na Amurka.
Mujallar Atlantic a cikin wani nazari mai taken "Ikon Yaƙi Yana Hannun Iran Kuma Trump Ya Cika Da Rudani Kuma Ya Nutsa Cikin Matsaloli Kuma An Wulakanta Shi," ta rubuta: Ikon yaƙin da ke tsakanin Amurka da Iran a yanzu yana hannun tsarin Iran ne, ba Donald Trump ba, kuma fahimtar juna da aka kulla kwanan nan, hasashe ne kawai da Trump ya kwallafa rai da shi, Iraniyawa sun wulakanta shi sau da yawa.