9 Yuli 2026 - 19:01
Source: ABNA24
IRGC: Sun Baje Cibiyar Kwamandancin Amurka A Yammacin Asiya Da Sansanin Sojan Sama Na Al-Azraq Na Jordan

Dakarun Juyin Musulunci na Iran a cikin wata sanarwa sun ba da rahoton murkushe cibiyar kwamandanci da sarrafawar makiya a Yammacin Asiya da sansanin sojan sama na makiya a Al-Azraq na Jordan da makamai masu linzami na ballastic guda 10.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya bayar da rahoton cewa: Dakarun Juyin Musulunci na Iran a ranar Alhamis 9 ga Yuli a cikin wata sanarwa sun rubuta: A sanarwar da ta gabata mun ce maimaita ta'addanci zai faɗaɗa martaninmu ga sauran sansanonin makiya a yankin, kuma a mataki na biyu na martani ga ta'addancin sojojin Amurka masu kashe yara, mun aiwatar da wannan barazana.

A ci gaban wannan sanarwa yazo cewa: Mayakan sararin samaniya na dakarun juyin musulunci da karfe 2:20 na yammacin yau, sun murkushe cibiyar kwamandanci da sarrafawar makiya a Yammacin Asiya da sansanin sojan saman makiya a Al-Azraq na Jordan da makamai masu linzami na ballastic guda 10.

Dakarun Juyin Musulunci a cikin sanarwarsu sun jaddada cewa: Idan aka maimaita ta'addancin sojojin ta'adda na Amurka, sauran sansanonin Amurka a yankin ba za su tsira daga wutar mu mai tsanani ba.

......................

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha