11 Yuli 2026 - 20:51
Source: ABNA24
Sojojin Isra'ila Sun Kona Garin Al-Khiyam A Kudancin Lebanon

Majiyoyin Lebanon sun tabbatar da aika-aikar sojojin Isra'ila na keta yarjejeniyar tsagaita wuta, inda suka shiga garin Al-Khiyam a Kudancin Lebanon, da gangan suka kona wasu sassansa.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Majiyoyin Lebanon sun ba da rahoton cewa sojojin Isra'ila sun gudanar da wani sabon aika-aika a garin Al-Khiyam da ke Kudancin Lebanon.

Sojojin Isra'ila sun shiga garin Al-Khiyam da ke yankin Marjayoun, kuma suka kona wasu sassan wurin da gangan. Majiyoyin da aka ambata sun kare cewa wannan mataki keta yarjejeniyar tsagaita wuta ce a fili. Mahukuntan Isra'ila kuwa ba su bayar da wata sanarwa a hukumance game da wannan lamarin ba tukuna.

...............

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha