12 Afirilu 2026 - 11:25
Source: ABNA24
Isra'ila Ta Jefa Bama-Baman Phosphorus A Yankuna 48 A Kudancin Lebanon 

Akalla a yankuna 48 da garuruwan da ke kudancin Lebanon sun sha ruwan bama-bamai da jiragen yakin sahyoniyawa tare da amfani da bama-baman da aka hana anfani da su na farin phosphorus a cikin sa'o'i 24 da suka gabata.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Akalla a yankuna 48 da garuruwan da ke kudancin Lebanon sun sha ruwan bama-bamai da jiragen yakin sahyoniyawa tare da amfani da bama-baman da aka hana anfani da su na farin phosphorus a cikin sa'o'i 24 da suka gabata.
A cewar wani rahoto na Arabi 21, jiragen yakin sahayoniyawa a cikin sa'o'i 24 da suka gabata sun kai hari kan yankuna 48, garuruwa, da gundumomi a kudancin Lebanon a hare-haren da suka kai na dabbanci. 
An kuma bayar da rahoton cewa, sun yi amfani da bama-bamai dauke da aka hana na farin phosphorus wajen wadannan hare-hare. Hare-haren dabbanci na gwamnatin Sahayoniya, wanda ya zama keta haddi bayan ayyana tsagaita wuta a yankin, ya yi sanadiyar shahadar mutane 27, ciki har da ma'aikatan ceto uku. A cikin wadannan hare-haren, Bint Jbeil, Sidon, Nabatieh, Kfar Sir, Toul, Zafta, da kauyuka da dama a kudancin Lebanon ne aka kaiws hari. 
Rahotanni daga kafafen yada labarai sun nuna cewa hare-haren sun haifar da tarin barna, musamman a cikin gidajen 'yan kasar Lebanon, biyo bayan wadannan hare-haren.

Your Comment

You are replying to: .
captcha