Kakakin ma'aikatar ilimi, ya ce yawan daliban da mugunyar Amurka da sahyoniyawa suka shahadantar a makarantar 'yan mata ta Shajreh Tayebeh Minab ya kai 165.
Ya kara da cewa: "Haka zalika, wannan hari na rashin mutuntaka da rashin imani na sahayoniyawan sun raunata wasu daliban wannan makaranta da adadinsu ya kai 95, wadanda dukkansu jami'an ceto suka kai su asibiti."
Wani mai magana da yawun ma'aikatar ilimi ya bayyana cewa: "Jiya, a cikin wani aiki na dabbanci da rashin mutuntaka da gwamnatin Sahayoniya ta kai hari (bam) wannan makarantar firamare ta 'yan mata har sau uku wacce makarantar tana dauke da adadin dalibai 264."
Ya kuma yi ishara da harin da gwamnatin Sahayoniyya ta kai wa wata makaranta a birnin Abbyek da ke Qazvin kuma ya ce: "A cikin wannan mummunan harin dabbanci na, makiya dalibi daya a makarantar ya yi shahada."
Your Comment