Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya ruwaito cewa: kungiyar Hizbullah ta Lebanon ta sanar a cikin wata sanarwa cewa dakarunta guda takwas sun yi shahada a harin da gwamnatin Isra'ila ta kai kan yankin Bekaa da ke gabashin Lebanon jiya (Juma'a).
Ma'aikatar Lafiya ta Lebanon ta kuma sanar a yau (Asabar) cewa mutane 10 sun yi shahada sannan 24 sun jikkata a hare-haren da gwamnatin Isra'ila ta kai a kudancin da gabashin Lebanon jiya.
Shahidan Da Kungiyar Hizbullah Ta Sanar A Kasar Labanon Sun Hada Da;
Kwamanda Shahid: Hussein Muhammad Yaghi "Abu Ali Sadeq"
Shahid Mujahid: Muhammad Ibrahim Al-Musawi "Ali Hussein"
Shahid Mujahid: Ali Zaid Al-Musawi "Nasser"
Shahid Mujahid: Hussein Khairullah Aala Al-Din "Ridwan"
Shahid Mujahid: Ahmed Hussein Al-Hajj Hassan "Mujahid"
Shahid Mujahid: Qasim Ali Mahdi "Abdul Muttalib"
Shahidi Mujahid: Ahmed Muhammad Zaaiter "Ashtar"
Shahid Mujahid: Hassanin Yasser Al-Sablani "Azab"

A halin da ake ciki, kafafen yada labarai na kasar Labanon a yau (Asabar) sun ba da sanarwar jana'izar shahidi Hussein Muhammad Yaghi da sahabbansa a kasar Lebanon ta hanyar buga hotunansu.
A cikin wannan sanarwar, Hizbullah bisa dogaro da ayar Alƙur'ani Mai Tsarki, ta kira waɗannan mutane da matsayin "shahidai na tafarkin Lebanon da al'ummarta" kuma sun jaddada cewa waɗannan dakarun sojoji da kwamandoji sun yi shahada sakamakon harin da Isra'ila ta kai wa yankin Bekaa na karshe.
Yawancin kafofin watsa labarai na Lebanon sun sanar da cewa jiragen yaƙin Isra'ila sun kai hare-hare a yankunan Bekaa da ke gabashin Lebanon a lokuta da dama a daren Juma'a.
.........................................
Your Comment