Amurka Bayan Ta Horas Da Dasa Jami’an Iraki Zata Fice Ta Koma Siriya Domin Aiwatar Da Iran Wannan Aiki

Pentagon Ta Mayar Da Hankali Kan Siriya Yayin Da Ta Ke Janye Sojojinta Daga Iraki
2 Oktoba 2025 - 11:45
Source: ABNA24
Amurka Bayan Ta Horas Da Dasa Jami’an Iraki Zata Fice Ta Koma Siriya Domin Aiwatar Da Iran Wannan Aiki

Wani babban jami'in tsaron Amurka ya sanar a jiya Laraba cewa, Amurka ta mika cikakken alhakin tsaron kasar ga gwamnatin Bagadaza, bisa yarjejeniyar da aka kulla a bara da gwamnatin Iraki.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlulbayt {As} –ABNA- ya bayar da rahoton cewa: Wani babban jami'in tsaron Amurka ya sanar a jiya Laraba cewa, Amurka ta mika cikakken alhakin tsaron kasar ga gwamnatin Bagadaza, bisa yarjejeniyar da aka kulla a bara da gwamnatin Iraki.

Jami'in da ba a bayyana sunansa ba ya fada a wata hira da jaridar The Hill cewa: "Sojojin Amurka sun fara mika alhakin mayar da martani ga barazanar tsaro daga jami’ansu zuwa dakarun Iraki".

Ya kara da cewa wadannan ayyuka za a bar su ne ga sojojin Iraqi da sojojin Amurka suka horar da su sama da shekaru goma.

Rahoton jaridar ya ce, Amurka ta karkata akalarta na soji daga tsaron Irakin zuwa karfafa zamanta a Siriya domin yakar barazanar ta'addanci. Ana sa ran za a tura wasu daga cikin sojojin da aka tura daga Iraki zuwa Erbil zuwa Syria nan gaba.

Idan dai ba a manta ba, ‘yan sa’o’i kadan kafin fara aikin rufe gwamnatin tarayya, ma’aikatar tsaron Amurka ta sanar da matakin rage yawan sojojin da take yi a kasar Iraki a wani bangare na abin da ta kira wani mataki na wucin gadi.

………….

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha