15 Nuwamba 2025 - 20:17
Source: ABNA24
Falasɗinu Ta Zamo Sabon Abun Koyin Gwagwarmaya Ga Ƙasashe Wajen Tunkarar Mulkin Mallakar Duniya

Wannan lokacin na "canzawar tarihi ne." Raguwar ikon mallakar ƙasashen yamma, farkawar ra'ayin jama'a, da kuma rawar da ƙasashe masu tasowa ke takawa na iya sake zana makomar tsarin duniya da makomar Falasɗinu. Gwagwarmayar Falasɗinu ba wai kawai wani labari ne na tarihi ba, sai dai ta samar da misali ga ƙasashe da ƙungiyoyi a duniya da ke wajen ikon mallakar ƙasashen yamma don yin tsayayya da tsarin jari-hujja, mulkin mallaka, da mulkin kama karya.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na AhlulBaiti (As) –ABNA-ya habarta cewa: Abubuwan da suke faruwa kwanan nan a Falasɗinu sun sake mayar da wannan ƙasa cibiyar ɗaya daga cikin rikice-rikice mafi sarkakiya a duniya.

Farfesa Martin Martinelli, farfesan tarihi a wannan zamani masanin tarihin Asiya da Afirka a Jami'ar Buenos Aires, ya yi imanin cewa Falasɗinawa sun jure wa tashin hankalin da ba a taɓa ganin irinsa ba wajen fuskantar Isra'ila, tun daga kakaba shiryayyiyar yunwar har zuwa kai hare-hare kai tsaye kan kafofin watsa labarai.

Wannan marubucin ɗan ƙasar Argentina kuma mai fafutukar adawa da Sahyuniya ya bayyana Falasɗinu a matsayin "babban ginshiƙin duniya a wajen fuskantar mulkin mallakar Yammacin duniya" in da ta ke fito na fito da gwagwarmaya wajen yaƙi da mulkin mallakar Isra'ila da wariyar launin fata.

Tsarin Kirkirar Labarin Isra'ila A Hukumance Yana Rugujewa

Martinelli yana ganin abubuwa uku ne ke taimakawa wajen wargaza ikon mallakar labarin Isra'ila: zanga-zangar duniya, buga hotuna da shaidu kai tsaye a shafukan sada zumunta, da kuma ƙoƙarin ƙasashe don gabatar da labaru masu zaman kansu. A cewarsa, kalmar "kisan kare dangi" yanzu ta sami damar yin amfani da kafofin watsa labarai da siyasa, kuma masana da yawa, gwamnatoci, da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa sun amince da ita.

Ƙungiyoyin Duniya Da Matsin Lamba A Aikace Sun Sami Damar Ƙalubalantar Isra'ila

Takunkumai da kauracewa da yajin aiki misalai ne na gaske na haɗin kan duniya akan wariyar launin fata ta Isra'ila. Yajin aikin tashar jiragen ruwa ta Italiya ya rikide ya zama yajin aiki a duk faɗin ƙasar ga Falasɗinu, wanda ke nuna cewa ƙungiyoyin duniya na iya sanya matsin lamba ga gwamnatin Isra'ila, kamar kauracewar da ta faru a lokacin mulkin wariyar launin fata a Afirka ta Kudu.

Ruhaniya Wani Ɓangare Ne Na Gwagwarmaya

Martinelli yana ɗaukar ruhaniyya a matsayin ɗaya daga cikin ginshiƙan gwagarmayar Falasɗinu, amma yana jaddada cewa babban batu anan ba rikicin addini ba ne; a maimakon haka batun ya kasance gwagwarmaya ce ta adawa da mulkin mallaka da kuma adawa da mulkin kama karya. Labarukan kasashen Yamma a hukumce suna ƙoƙarin bayyana wannan takaddama a matsayin tashin hankali na addini ko al'adu, yayin da tushen rikicin ya ta'allaka ne a cikin manufofin Isra'ila na raba al'umma da haɓaka tasirin Yamma a yankin.

Wannan Lokacin Tarihi Zai Iya Canza Yanayin Tsarin Duniya Da Falasɗinu Na Gaba

A ganinsa, wannan lokacin na "canzawar tarihi ne." Raguwar ikon mallakar ƙasashen yamma, farkawar ra'ayin jama'a, da kuma rawar da ƙasashe masu tasowa ke takawa na iya sake zana makomar tsarin duniya da makomar Falasɗinu. Gwagwarmayar Falasɗinu ba wai kawai wani labari ne na tarihi ba, sai dai ta samar da misali ga ƙasashe da ƙungiyoyi a duniya da ke wajen ikon mallakar ƙasashen yamma don yin tsayayya da tsarin jari-hujja, mulkin mallaka, da mulkin kama karya.

Your Comment

You are replying to: .
captcha