Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarto cewa: Wannan ziyarar ta zo ne a lokacin da, baya ga tattaunawa kan ci gaban tsarin tsaron sama da jiragen yaƙi na F-35, mafi mahimmancin abin da za a mayar da hankali a kai shi ne sanya hannu kan yarjejeniyar tarihi don haɗin gwiwar makamashin nukiliya tsakanin ƙasashen biyu.
Saudiyya, a matsayinta na babbar ƙasar da ke fitar da mai a duniya kuma babbar ƙasa mai ƙarfin tattalin arziki a Gabas ta Tsakiya, ta daɗe tana neman samun fasahar makamashin nukiliya na zaman lafiya tare da haɗin gwiwar Amurka. Wannan batu a da yana cikin tattaunawar daidaita dangantaka tsakanin Riyadh da Tel Aviv, amma bayan ci gaban yaƙin Gaza, yanzu an sanya shi a cikin ajandar kaitsaye.
Your Comment