Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarto cewa: Ci gaban fagen yaki da siyasa a Iraki da Siriya ya shiga wani muhimmin mataki wanda zai iya canza daidaiton iko a yankin. A irin wannan yanayi, Sayyid Mohammad Jawad Hosseini, wani mai sharhi na ƙasa da ƙasa, ya yi gargaɗi a cikin wata sanarwa da ke bayyana yiwuwar faruwar wani yanayi anan gaba game da sakamakon mataki da Amurka da Iran za su ɗauka; sakamakon da zai iya kawo tsaro da tsarin siyasa na Iraki kusa da wani muhimmin matsayi har ma ya kai ga rugujewarsa.
Rubutun wannan bayanin nasa yazo kamar haka:
Wani muhimmin batu da dole ne a yi la'akari da shi shine sakamakon da zai haifar da mataki na gaba da Amurka da Iran za su ɗauka a Iraki da Siriya.
Mataki mai mahimmanci ga makomar yankin
Za a kai wa Rundunar Jama'a (Hashdush Sha’abi) da shugabannin siyasa da ke kusa da gwagwarmaya hari, da kuma albarkatun soja da tattalin arziki.
Za a aiwatar da kawar da kwamandoji da mutane masu tasiri a zahiri kamar Qais al-Khazali, Akram al-Kaabi, al-Mohammaddawy, Hadi al-Amiri, Nouri al-Maliki da sauran mutane masu tasiri.
Za a kai hari kan kayayyakin more rayuwa na Hashdush Sha’abi da Kata’ib da Hizbullah.
Wannan daidai yake da yanayin da ya faru ga Hizbullah, Hamas, Yemen da Iran, kuma za mu gan shi a Iraki.
An yi hasashen wani bala'i da zai kawo yanayin cikin gida a Iraki zuwa ga rugujewa, kamar a Lebanon, kuma ya nuna babban rashin daidaiton kwance damarar makamai.
Iraƙi ita ce sansanin soja na ƙarshe kuma mafi mahimmanci ga Tehran, sai dai idan Tehran ta yi abin da ya saba wa dabarunta na tsaro na shekaru biyu da suka gabata ya zamo sabon yaƙi ya faru a Iraki da Siriya.
Za a kammala cimma burin Amurka da Isra'ila a Siriya ta hanyar kwance damarar makamai gaba ɗaya na ƙungiyoyin gwagwarmaya na Iraki, canje-canjen siyasa da ƙarfafa ƙungiyoyin kawance. Bugu da ƙari, raunin tasirin Turkiyya shi ma zai kasance a cikin ajandar.
Yana da matuƙar muhimmanci a san abin da zai faru a gaba da kuma abin da sakamakon zai kasance.
Your Comment