16 Nuwamba 2025 - 11:22
Source: ABNA24
Ƙasashen Yammacin Duniya Za Su Kirkiro Sabbin Ka'idoji Don Sa’idon Masu Kula IAEA A Iran

Kafar yada labarai ta Amurka Bloomberg ta ruwaito cewa kasashen Yamma na shirin samar da sabbin ka'idoji don sa ido kan masu kula da su a Iran a taron da za a yi na Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya; batun da ya shafi matsayin ma'ajiyar uranium da aka inganta bayan hare-haren jiragen sama na Amurka da Isra’ila.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarto cewa: jami'ai uku na kasashen Yamma sun shaida wa Bloomberg bisa sharadin boye sunansu cewa kasashen Yamma za su samar da sabbin ka'idoji ga masu kula da IAEA a Iran a taron Kwamitin Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya da za a gudanar daga 19 zuwa 20 ga Nuwamba.

Wannan taron ana gudanar da shi ne a wani yanayi da, bayan karewar kuduri mai lamba 2231 na Majalisar Tsaro a watan Oktoba, an cire batun sa ido kan aiwatar da yarjejeniyar nukiliya ta Iran a karkashin wannan kuduri daga ajandar Hukumar.

Iran Ta Dakatar Da Haɗakar Aiki Da IAEA

Iran Ta Dakatar aiki tare da IAEA Bayan Harin Jiragen Saman Amurka Da Isra'ila Kan Makamashin Nukiliyarta A Watan Yuni. Duk da haka, an amince da wani sabon tsari na haɗin gwiwa daga baya a Masar, wanda zai ba masu duba damar yin amfani da wasu wurare, ban da wuraren da aka jefa bama-bamai a Isfahan, Fordow da Natanz.

Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya ta yi hasashen wurin da tarin uranium  mai yawa ya kasance tun bayan hare-haren. Jami'an Iran sun ce sinadarai an binne su a ƙarƙashin tarkacen wuraren da aka jefa bama-bamai. Jami'an diflomasiyyar ƙasashen yamma sun yi gargaɗin cewa ko da tare da cikakken haɗin gwiwar Iran, zai iya ɗaukar shekaru kafin a sake gina aminci game da makomar sinadaran.

Rashin Jituwa Tsakanin Ƙasashen Yamma

Bloomberg ta rubuta: Wasu ƙasashen Yamma suna neman ƙara matsin lamba ga Iran ta hanyar iyakance haɗin gwiwar fasahar IAEA a fannoni kamar magungunan nukiliya, yayin da wasu suka yi gargaɗin cewa irin wannan matakin zai iya haifar da koma baya da kuma ƙara yiwuwar janyewar Iran daga yarjejeniyar hana yaɗuwar makaman nukiliya.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha