Iran Ta Dakatar Da Jirgin Ruwan Dakon Mai A Mashigin Hormuz

Rundunar Sojojin Juyin Juya Halin Iran (IRGC) Ta Tabbatar Da Kama Jirgin.
15 Nuwamba 2025 - 19:01
Source: ABNA24
Iran Ta Dakatar Da Jirgin Ruwan Dakon Mai A Mashigin Hormuz

Rundunar Sojin Ruwan Iran Ta Kama Wani jirgin ruwan dakon Mai Dauke Da Tan 30,000 Na Man Fetur A Mashigin Hormuz.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na AhlulBaiti (As) –ABNA-ya habarta cewa: Rundunar Sojin Ruwan Iran ta tabbatar da kwace wani jirgin ruwa mai dauke da mai wanda ya karya dokokin kasa da kasa a Tekun Oman.

Rundunar Sojojin Juyin Juya Halin Iran (IRGC) Ta Tabbatar ta sanar da cewa ta kwace wani jirgin ruwa mai dauke da tutar Marshall Islands jiya da safe. Jirgin yana dauke da tan 30,000 na sinadarai masu guba ba bisa ka'ida ba.

Jirgin ruwan yana kan hanyarsa daga masarautar Ajman ta Singapore zuwa Hadaddiyar Daular Larabawa.

A halin yanzu, Rundunar Sojojin Ruwa ta Amurka ta bayyana cewa tana sake duba lamarin game da kwace jirgin ruwan mai da Iran ta yi.

Your Comment

You are replying to: .
captcha