6 Yuli 2025 - 21:38
Source: ABNA24
Katsina Najeriya: An Gudanar Da Muzaharar Ashura + Hotuna 

Da misalin ƙarfe 4:00pm na yammacin yau Lahadi 10 ga watan Muharrama, 1447 dai-dai da 06/07/2025 ne ’yan’uwa musulmi almajiran Sayyid Zakzaky (H) na Da’irar Katsina suka fito ƙwai da kwarkwata domin bin sahun muminai na faɗin duniya mabiya mazhabar Ahlulbaiti (S) wajan nuna alhini da juyayi na kisan jikan Annabi Muhamamd, Imamul Husain (A.S).

Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul Baity (As) -Abna- ya bayar da rahoton cewa: Muzaharar ta ci gaba da gudana lami lafiya, inda ’yan’uwa Maza da mata sanyen da baƙaƙen kaya, ke rera waƙoƙin juyayi da kuma ɗaga totoci masu rubutun “Ya Husain” ko “Labbaika Ya Hussain” ...

A gaban Muzaharar, tsakiya da kuma karshenta Harisawa ne masu kula da tsari, nizami, sahu da kuma ƙa'idar hanya, inda suke kula da ababen hawa da basu hanya domin wucewa ba tare da an samu cinkoso ko haɗari ba.

Ga wasu hotuna da aka ɗauka a yanzu haka:

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha