Da misalin ƙarfe 9:00 na safiyar Talatar 12 ga watan Rabi’ul Awwal, 1448H, wanda ya yi daidai da 25 ga watan Agusta, 2026, ’yan’uwa Musulmi almajiran Sayyid Ibrahim Zakzaky (H) na garin Katsina suka fito ƙwai da kwarkwata don nuna murnarsu da zagayowar ranar haihuwar Manzon Rahma (S).
Duk abin da za mu yi saboda Manzon Allah (SAWW), to ba mu yi komai ba. Ko da ma ba za a ba mu lada ba, Manzon Allah (SAWW) ya cancanci mu yi murna da samuwarsa, domin Allah (SWT) yana son Manzon sa, mu ma muna son sa. Saboda haka, gashi nan, muna yi, ko ba a ba mu lada ba, mun taya Allah aiki. Kuma wallahi, da Allah (SWT) bai son wannan abin (Maulud) da muke yi, da tuni an bari… da tuni an bar shi. Domin Allah yana kishin Manzon sa sosai.