Jiya laraba 23 ga watan DhulQa'ada, 1446H (21/05/2025) Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), kamar yadda aka saba kowacce shekara ya gana da wasu daga cikin ɗaliban makarantun Fudiyya daban-daban waɗanda suke shirin yin bikin haddar Alkur’ani Mai girma, a gidansa da ke Abuja.
A ranar Laraba 16 ga Zulqa’ada, 1446 (14/5/2025) Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya gana da ‘yan uwa 25 wadanda aka saki daga cikin mutum kimanin 60 da ake tsare da su a kurkukun Kuje da ke Abuja, tun bayan waki’ar 22 July 2019.