Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: "Talia Lankeri," tsohuwar Shugabar Majalisar Tsaron Isra'ila, tayi ikrarin cewa gwamnatin ta fuskanci gazawar leken asiri a lokacin harin Hamas a ranar 7 ga Oktoba. "Dole ne mu yarda da gazawar leken asiri a harin 7 ga Oktoba da Hamas ta kai".
Lankeri, wacce tana cikin bita da fidda darussan da suk koya bayan aikin harin gwagwarmaya, ta kara da cewa: "Harin na 7 ga Oktoba ba wai kawai bala'i ne na ƙasa wanda ba a taɓa ganin irinsa ba, kai har ma ya kasance wani lokaci ne mai mahimmanci wanda ke buƙatar cikakken binciken ƙwararru da na ilimi game da hanyoyin yanke shawara a matakan siyasa da tsaro." Ta ci gaba da jaddada cewa: "Gazawar asali ta Isra'ila ta ta'allaka ne a cikin tushenta wanda ya saɓa wa dukkan ƙa'idodin tsaro na ƙwararru".
Your Comment