ABNA24 : Kakakin hukumar abinci da magunguna na kasar Iran Kianush Jahanpur ne ya sanar da hakan cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter inda ya ce: Ya zuwa yanzu dai magungunan rigakafin da Iran ta samar guda biyar ne suka shiga cikin jerin magungunan rigakafin cutar COVID-19 da hukumar lafiya ta duniya ta amince da su.
Tun a kwanakin baya ne dai Iran ta samar da wadannan magunguna na rigakafin da kuma gabatar da su ga cibiyoyin kasa da kasa din don kara tantance su wanda a halin yanzu hukumar kula da lafiya ta duniya ta amince da biyar daga cikinsu da kuma sanya su cikin jerin sunayen rigakafin da ta amince da su.
Tun bayan bullar wannan annoba ta korona ne dai masana da likitocin Iran suka dukufa wajen samar da magani da kuma rigakafin wannan cutar wacce ta yi sanadiyyar mutuwar wani adadi mai yawa na al’ummomi duniya ciki kuwa har da kasar ta Iran.
342/